Romans 10

1‘Yan’uwana, muradin zuciyata da dukkan addu’oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton. 2Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba. 3Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba.

4Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata. 5Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari’a: ‘’mutumin da ya aikata adalcin shari’a, zai rayu ta wurin wannan adalcin.‘’

6Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, ‘’Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?‘’(don ya sauko da Almasihu kasa). 7Kada ku ce, ‘’Wa zai gangara zuwa kasa?‘’ (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu).

8Amma me yake cewa? “kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka.” Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa. 9Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.

11Don nassi na cewa, ‘’Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,‘’ 12Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba‘al’ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi. 13Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.

14To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba? 15Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa’azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa’azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, “Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!”

16Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, ‘’Ubangiji, wa ya gaskata da sakon? 17Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu.

18Amma na ce, “ko basu ji ba ne? I, tabbas‘’ muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya.‘’

19yau, na ce, ‘’Ko Isra’ila basu sani ba ne?‘’ Da farko Musa ya ce, “Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al’umma ba. Abin da nake nufi nan shine al’ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali.‘’

20Amma Ishaya da karfin hali ya ce, ‘’Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba. ‘’Amma ga Isra’ila kam ya ce, ‘’ na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai.‘’

21

Copyright information for HauULB